Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 231 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿وَإِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ سَرِّحُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖۚ وَلَا تُمۡسِكُوهُنَّ ضِرَارٗا لِّتَعۡتَدُواْۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ وَلَا تَتَّخِذُوٓاْ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ هُزُوٗاۚ وَٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَمَآ أَنزَلَ عَلَيۡكُم مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡحِكۡمَةِ يَعِظُكُم بِهِۦۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ ﴾
[البَقَرَة: 231]
﴿وإذا طلقتم النساء فبلغن أجلهن فأمسكوهن بمعروف أو سرحوهن بمعروف ولا تمسكوهن﴾ [البَقَرَة: 231]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma idan kun saki mata, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alheri ko ku sallame su da alheri, kuma kada ku riƙe su a kan cutarwa domin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙiƙa, ya zalunci kansa. Kuma kada ku riƙi ayoyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littafi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kome Masani ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan kun saki mata, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alheri ko ku sallame su da alheri, kuma kada ku riƙe su a kan cutarwa domin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙiƙa, ya zalunci kansa. Kuma kada ku riƙi ayoyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littafi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kome Masani ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne |