×

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu'ãmalar bãyar da 2:282 Hausa translation

Quran infoHausaSurah Al-Baqarah ⮕ (2:282) ayat 282 in Hausa

2:282 Surah Al-Baqarah ayat 282 in Hausa (الهوسا)

Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 282 - البَقَرَة - Page - Juz 3

﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا تَدَايَنتُم بِدَيۡنٍ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى فَٱكۡتُبُوهُۚ وَلۡيَكۡتُب بَّيۡنَكُمۡ كَاتِبُۢ بِٱلۡعَدۡلِۚ وَلَا يَأۡبَ كَاتِبٌ أَن يَكۡتُبَ كَمَا عَلَّمَهُ ٱللَّهُۚ فَلۡيَكۡتُبۡ وَلۡيُمۡلِلِ ٱلَّذِي عَلَيۡهِ ٱلۡحَقُّ وَلۡيَتَّقِ ٱللَّهَ رَبَّهُۥ وَلَا يَبۡخَسۡ مِنۡهُ شَيۡـٔٗاۚ فَإِن كَانَ ٱلَّذِي عَلَيۡهِ ٱلۡحَقُّ سَفِيهًا أَوۡ ضَعِيفًا أَوۡ لَا يَسۡتَطِيعُ أَن يُمِلَّ هُوَ فَلۡيُمۡلِلۡ وَلِيُّهُۥ بِٱلۡعَدۡلِۚ وَٱسۡتَشۡهِدُواْ شَهِيدَيۡنِ مِن رِّجَالِكُمۡۖ فَإِن لَّمۡ يَكُونَا رَجُلَيۡنِ فَرَجُلٞ وَٱمۡرَأَتَانِ مِمَّن تَرۡضَوۡنَ مِنَ ٱلشُّهَدَآءِ أَن تَضِلَّ إِحۡدَىٰهُمَا فَتُذَكِّرَ إِحۡدَىٰهُمَا ٱلۡأُخۡرَىٰۚ وَلَا يَأۡبَ ٱلشُّهَدَآءُ إِذَا مَا دُعُواْۚ وَلَا تَسۡـَٔمُوٓاْ أَن تَكۡتُبُوهُ صَغِيرًا أَوۡ كَبِيرًا إِلَىٰٓ أَجَلِهِۦۚ ذَٰلِكُمۡ أَقۡسَطُ عِندَ ٱللَّهِ وَأَقۡوَمُ لِلشَّهَٰدَةِ وَأَدۡنَىٰٓ أَلَّا تَرۡتَابُوٓاْ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً حَاضِرَةٗ تُدِيرُونَهَا بَيۡنَكُمۡ فَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَلَّا تَكۡتُبُوهَاۗ وَأَشۡهِدُوٓاْ إِذَا تَبَايَعۡتُمۡۚ وَلَا يُضَآرَّ كَاتِبٞ وَلَا شَهِيدٞۚ وَإِن تَفۡعَلُواْ فَإِنَّهُۥ فُسُوقُۢ بِكُمۡۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱللَّهُۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ ﴾
[البَقَرَة: 282]

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu'ãmalar bãyar da bãshi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubũta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubũtu a tsakaninku da ãdalci. Kuma kada marubũci ya ki rubũtãwa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubũta. Kuma wanda bãshin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsõron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bãshin yake a kansa yã kasance wãwã ne kõ kuwa rarrauna, kõ kuwa shi bã ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da ãdalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mãtã biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun dõmin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazãkũtar* da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙõsa ga rubũta shi, ƙarami ya kasance kõ babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi ãdalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gẽwayarwa da shi hannu da hannu a tsakãninku to bãbu laifi a kanku, ya zama ba ku rubũta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fãsiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kõme Masani ne

❮ Previous Next ❯

ترجمة: ياأيها الذين آمنوا إذا تداينتم بدين إلى أجل مسمى فاكتبوه وليكتب بينكم, باللغة الهوسا

﴿ياأيها الذين آمنوا إذا تداينتم بدين إلى أجل مسمى فاكتبوه وليكتب بينكم﴾ [البَقَرَة: 282]

Abubakar Mahmood Jummi
Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan kun yi mu'amalar bayar da bashi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubuta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubutu a tsakaninku da adalci. Kuma kada marubuci ya ki rubutawa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubuta. Kuma wanda bashin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsoron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bashin yake a kansa ya kasance wawa ne ko kuwa rarrauna, ko kuwa shi ba ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da adalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mata biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun domin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazakutar* da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙosa ga rubuta shi, ƙarami ya kasance ko babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi adalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gewayarwa da shi hannu da hannu a tsakaninku to babu laifi a kanku, ya zama ba ku rubuta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fasiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kome Masani ne
Abubakar Mahmoud Gumi
Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan kun yi mu'amalar bayar da bashi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubuta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubutu a tsakaninku da adalci. Kuma kada marubuci ya ki rubutawa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubuta. Kuma wanda bashin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsoron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bashin yake a kansa ya kasance wawa ne ko kuwa rarrauna, ko kuwa shi ba ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da adalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mata biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun domin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazakutar da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙosa ga rubuta shi, ƙarami ya kasance ko babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi adalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gewayarwa da shi hannu da hannu a tsakaninku to babu laifi a kanku, ya zama ba ku rubuta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fasiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kome Masani ne
Abubakar Mahmoud Gumi
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu'ãmalar bãyar da bãshi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubũta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubũtu a tsakaninku da ãdalci. Kuma kada marubũci ya ki rubũtãwa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubũta. Kuma wanda bãshin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsõron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bãshin yake a kansa yã kasance wãwã ne kõ kuwa rarrauna, kõ kuwa shi bã ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da ãdalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mãtã biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun dõmin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazãkũtar da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙõsa ga rubũta shi, ƙarami ya kasance kõ babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi ãdalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gẽwayarwa da shi hannu da hannu a tsakãninku to bãbu laifi a kanku, ya zama ba ku rubũta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fãsiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kõme Masani ne
❮ Previous Next ❯

Verse in more languages

Transliteration Bangla Bosnian German English Persian French Hindi Indonesian Kazakh Dutch Russian Spanish Turkish Urdu Uzbek