Quran with Hausa translation - Surah An-Nur ayat 61 - النور - Page - Juz 18
﴿لَّيۡسَ عَلَى ٱلۡأَعۡمَىٰ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡأَعۡرَجِ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرِيضِ حَرَجٞ وَلَا عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۡ أَن تَأۡكُلُواْ مِنۢ بُيُوتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ ءَابَآئِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أُمَّهَٰتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ إِخۡوَٰنِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أَخَوَٰتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أَعۡمَٰمِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ عَمَّٰتِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ أَخۡوَٰلِكُمۡ أَوۡ بُيُوتِ خَٰلَٰتِكُمۡ أَوۡ مَا مَلَكۡتُم مَّفَاتِحَهُۥٓ أَوۡ صَدِيقِكُمۡۚ لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَأۡكُلُواْ جَمِيعًا أَوۡ أَشۡتَاتٗاۚ فَإِذَا دَخَلۡتُم بُيُوتٗا فَسَلِّمُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۡ تَحِيَّةٗ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ مُبَٰرَكَةٗ طَيِّبَةٗۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ ﴾
[النور: 61]
﴿ليس على الأعمى حرج ولا على الأعرج حرج ولا على المريض حرج﴾ [النور: 61]
Abubakar Mahmood Jummi Babu laifi a kan makaho, kuma babu laifi a kan gurgu, kuma babu laifi a kan majiyyaci, kuma babu laifi a kan kowanenku, ga ku ci (abinci) daga gidajenku, ko daga gidajen ubanninku, ko daga gidajen uwayenku, ko daga gidajen 'yan'uwanku maza, ko daga gidajen 'yan'uwanku mata, ko daga gidajen baffanninku, ko daga gidajen gwaggwanninku, ko daga gidajen kawunnanku, ko daga gidajen innoninku ko abin da kuka mallaki mabuɗansa ko abokinku babu laifi a gare ku ku ci gaba ɗaya, ko dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidaje, ku yi sallama a kan kawunanku,* gaisuwa ta daga wurin Allah mai albarka, mai daɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku ku yi hankali |
Abubakar Mahmoud Gumi Babu laifi a kan makaho, kuma babu laifi a kan gurgu, kuma babu laifi a kan majiyyaci, kuma babu laifi a kan kowanenku, ga ku ci (abinci) daga gidajenku, ko daga gidajen ubanninku, ko daga gidajen uwayenku, ko daga gidajen 'yan'uwanku maza, ko daga gidajen 'yan'uwanku mata, ko daga gidajen baffanninku, ko daga gidajen gwaggwanninku, ko daga gidajen kawunnanku, ko daga gidajen innoninku ko abin da kuka mallaki mabuɗansa ko abokinku babu laifi a gare ku ku ci gaba ɗaya, ko dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidaje, ku yi sallama a kan kawunanku, gaisuwa ta daga wurin Allah mai albarka, mai daɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku ku yi hankali |
Abubakar Mahmoud Gumi Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku, gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali |