Quran with Hausa translation - Surah An-Nur ayat 62 - النور - Page - Juz 18
﴿إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَإِذَا كَانُواْ مَعَهُۥ عَلَىٰٓ أَمۡرٖ جَامِعٖ لَّمۡ يَذۡهَبُواْ حَتَّىٰ يَسۡتَـٔۡذِنُوهُۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَسۡتَـٔۡذِنُونَكَ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۚ فَإِذَا ٱسۡتَـٔۡذَنُوكَ لِبَعۡضِ شَأۡنِهِمۡ فَأۡذَن لِّمَن شِئۡتَ مِنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمُ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ ﴾
[النور: 62]
﴿إنما المؤمنون الذين آمنوا بالله ورسوله وإذا كانوا معه على أمر جامع﴾ [النور: 62]
Abubakar Mahmood Jummi Waɗanda ke muminai sosai, su ne waɗanda suka yi imani da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tare da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, ba su tafiya sai sun neme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan su ne suke yin imani da Allah da ManzonSa. To, idan sun neme ka izni saboda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nema musu gafara daga Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗanda ke muminai sosai, su ne waɗanda suka yi imani da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tare da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, ba su tafiya sai sun neme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan su ne suke yin imani da Allah da ManzonSa. To, idan sun neme ka izni saboda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nema musu gafara daga Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗanda ke mũminai sõsai, su ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tãre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bã su tafiya sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke yin ĩmãni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabõda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmã musu gãfara daga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai |