Quran with Hausa translation - Surah al-‘Imran ayat 7 - آل عِمران - Page - Juz 3
﴿هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ مِنۡهُ ءَايَٰتٞ مُّحۡكَمَٰتٌ هُنَّ أُمُّ ٱلۡكِتَٰبِ وَأُخَرُ مُتَشَٰبِهَٰتٞۖ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمۡ زَيۡغٞ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَٰبَهَ مِنۡهُ ٱبۡتِغَآءَ ٱلۡفِتۡنَةِ وَٱبۡتِغَآءَ تَأۡوِيلِهِۦۖ وَمَا يَعۡلَمُ تَأۡوِيلَهُۥٓ إِلَّا ٱللَّهُۗ وَٱلرَّٰسِخُونَ فِي ٱلۡعِلۡمِ يَقُولُونَ ءَامَنَّا بِهِۦ كُلّٞ مِّنۡ عِندِ رَبِّنَاۗ وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّآ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ ﴾
[آل عِمران: 7]
﴿هو الذي أنـزل عليك الكتاب منه آيات محكمات هن أم الكتاب وأخر﴾ [آل عِمران: 7]
Abubakar Mahmood Jummi Shi ne wanda ya saukar da Littafi a gare ka, daga cikinsa akwai ayoyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littafin, da wasu masu kama da juna. To, amma waɗanda yake a cikin zukatansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kama da juna daga gare shi, domin neman yin fitina da tawilinsa. Kuma babu wanda ya san tawilinsaface Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi suna cewa: "Mun yi imani da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma babu mai tunani face ma'abuta hankula |
Abubakar Mahmoud Gumi Shi ne wanda ya saukar da Littafi a gare ka, daga cikinsa akwai ayoyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littafin, da wasu masu kama da juna. To, amma waɗanda yake a cikin zukatansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kama da juna daga gare shi, domin neman yin fitina da tawilinsa. Kuma babu wanda ya san tawilinsaface Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi suna cewa: "Mun yi imani da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma babu mai tunani face ma'abuta hankula |
Abubakar Mahmoud Gumi Shi ne wanda ya saukar da Littãfi a gare ka, daga cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littãfin, da wasu mãsu kamã da jũna. To, amma waɗanda yake a cikin zukãtansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kamã da jũna daga gare shi, dõmin nẽman yin fitina da tãwĩlinsa. Kuma bãbu wanda ya san tãwĩlinsafãce Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi sunã cẽwa: "Mun yi ĩmãni da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abũta hankula |