Quran with Hausa translation - Surah Al-Ahzab ayat 4 - الأحزَاب - Page - Juz 21
﴿مَّا جَعَلَ ٱللَّهُ لِرَجُلٖ مِّن قَلۡبَيۡنِ فِي جَوۡفِهِۦۚ وَمَا جَعَلَ أَزۡوَٰجَكُمُ ٱلَّٰٓـِٔي تُظَٰهِرُونَ مِنۡهُنَّ أُمَّهَٰتِكُمۡۚ وَمَا جَعَلَ أَدۡعِيَآءَكُمۡ أَبۡنَآءَكُمۡۚ ذَٰلِكُمۡ قَوۡلُكُم بِأَفۡوَٰهِكُمۡۖ وَٱللَّهُ يَقُولُ ٱلۡحَقَّ وَهُوَ يَهۡدِي ٱلسَّبِيلَ ﴾
[الأحزَاب: 4]
﴿ما جعل الله لرجل من قلبين في جوفه وما جعل أزواجكم اللائي﴾ [الأحزَاب: 4]
Abubakar Mahmood Jummi Allah bai sanya zuciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya matanku waɗanda kuke yin zihari daga gare su, su zama uwayenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankakarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu naku, maganarku ce da bakunanku alhali kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shi ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai |
Abubakar Mahmoud Gumi Allah bai sanya zuciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya matanku waɗanda kuke yin zihari daga gare su, su zama uwayenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankakarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu naku, maganarku ce da bakunanku alhali kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shi ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai |
Abubakar Mahmoud Gumi Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mãtanku waɗanda kuke yin zihãri daga gare su, su zama uwãyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankãkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu nãku, maganarku ce da bãkunanku alhãli kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai |