Quran with Hausa translation - Surah An-Nisa’ ayat 127 - النِّسَاء - Page - Juz 5
﴿وَيَسۡتَفۡتُونَكَ فِي ٱلنِّسَآءِۖ قُلِ ٱللَّهُ يُفۡتِيكُمۡ فِيهِنَّ وَمَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ فِي يَتَٰمَى ٱلنِّسَآءِ ٱلَّٰتِي لَا تُؤۡتُونَهُنَّ مَا كُتِبَ لَهُنَّ وَتَرۡغَبُونَ أَن تَنكِحُوهُنَّ وَٱلۡمُسۡتَضۡعَفِينَ مِنَ ٱلۡوِلۡدَٰنِ وَأَن تَقُومُواْ لِلۡيَتَٰمَىٰ بِٱلۡقِسۡطِۚ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِهِۦ عَلِيمٗا ﴾
[النِّسَاء: 127]
﴿ويستفتونك في النساء قل الله يفتيكم فيهن وما يتلى عليكم في الكتاب﴾ [النِّسَاء: 127]
Abubakar Mahmood Jummi Suna yi maka fatawa a cikin sha'anin mata. Ka ce: "Allah Yana bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantawa a kanku a cikin Littafi, a cikin sha'anin marayun mata waɗanda ba ku ba su abin da aka rubuta musu* (na gado) ba, kuma kuna kwaɗayin ku aure su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yara, da sha'anin tsayuwarku ga marayu da adalci. Kuma abin da kuka aikata daga alheri, to, lalle ne, Allah Ya kasance Masani a gare shi |
Abubakar Mahmoud Gumi Suna yi maka fatawa a cikin sha'anin mata. Ka ce: "Allah Yana bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantawa a kanku a cikin Littafi, a cikin sha'anin marayun mata waɗanda ba ku ba su abin da aka rubuta musu (na gado) ba, kuma kuna kwaɗayin ku aure su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yara, da sha'anin tsayuwarku ga marayu da adalci. Kuma abin da kuka aikata daga alheri, to, lalle ne, Allah Ya kasance Masani a gare shi |
Abubakar Mahmoud Gumi Sunã yi maka fatawa a cikin sha'anin mãtã. Ka ce: "Allah Yanã bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantãwa a kanku a cikin Littãfi, a cikin sha'anin marãyun mãtã waɗanda ba ku bã su abin da aka rubũta musu (na gãdo) ba, kuma kunã kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yãra, da sha'anin tsayuwarku ga marãyu da ãdalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yã kasance Masani a gare shi |