Quran with Hausa translation - Surah An-Nisa’ ayat 77 - النِّسَاء - Page - Juz 5
﴿أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ قِيلَ لَهُمۡ كُفُّوٓاْ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقِتَالُ إِذَا فَرِيقٞ مِّنۡهُمۡ يَخۡشَوۡنَ ٱلنَّاسَ كَخَشۡيَةِ ٱللَّهِ أَوۡ أَشَدَّ خَشۡيَةٗۚ وَقَالُواْ رَبَّنَا لِمَ كَتَبۡتَ عَلَيۡنَا ٱلۡقِتَالَ لَوۡلَآ أَخَّرۡتَنَآ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖۗ قُلۡ مَتَٰعُ ٱلدُّنۡيَا قَلِيلٞ وَٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّمَنِ ٱتَّقَىٰ وَلَا تُظۡلَمُونَ فَتِيلًا ﴾
[النِّسَاء: 77]
﴿ألم تر إلى الذين قيل لهم كفوا أيديكم وأقيموا الصلاة وآتوا الزكاة﴾ [النِّسَاء: 77]
| Abubakar Mahmood Jummi Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bayar da zakka."? To a lokacin da aka wajabta musu yaƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu suna tsoron mutane kamar tsoron Allah ko kuwa mafi tsanani ga tsoron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yaƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin daɗin duniya kaɗan ne, kuma Lahira ce mafi alheri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ba a zaluntar ku da sililin hancin gurtsun dabino |
| Abubakar Mahmoud Gumi Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bayar da zakka."? To a lokacin da aka wajabta musu yaƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu suna tsoron mutane kamar tsoron Allah ko kuwa mafi tsanani ga tsoron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yaƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin daɗin duniya kaɗan ne, kuma Lahira ce mafi alheri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ba a zaluntar ku da sililin hancin gurtsun dabino |