Quran with Hausa translation - Surah An-Nisa’ ayat 81 - النِّسَاء - Page - Juz 5
﴿وَيَقُولُونَ طَاعَةٞ فَإِذَا بَرَزُواْ مِنۡ عِندِكَ بَيَّتَ طَآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ غَيۡرَ ٱلَّذِي تَقُولُۖ وَٱللَّهُ يَكۡتُبُ مَا يُبَيِّتُونَۖ فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلًا ﴾
[النِّسَاء: 81]
﴿ويقولون طاعة فإذا برزوا من عندك بيت طائفة منهم غير الذي تقول﴾ [النِّسَاء: 81]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma suna cewa, "Da'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwana da niyyar wanin abin da take faɗa, alhali kuwa Allah na rubuta abin da suke kwana da niyyarsa. Saboda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dogara ga Allah, kuma Allah Ya isa ya zama wakili |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma suna cewa, "Da'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwana da niyyar wanin abin da take faɗa, alhali kuwa Allah na rubuta abin da suke kwana da niyyarsa. Saboda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dogara ga Allah, kuma Allah Ya isa ya zama wakili |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma sunã cẽwa, "Dã'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwãna da niyyar wanin abin da take faɗa, alhãli kuwa Allah na rubũta abin da suke kwãna da niyyarsa. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dõgara ga Allah, kuma Allah Yã isa ya zama wakĩli |