Quran with Hausa translation - Surah Al-Fath ayat 15 - الفَتح - Page - Juz 26
﴿سَيَقُولُ ٱلۡمُخَلَّفُونَ إِذَا ٱنطَلَقۡتُمۡ إِلَىٰ مَغَانِمَ لِتَأۡخُذُوهَا ذَرُونَا نَتَّبِعۡكُمۡۖ يُرِيدُونَ أَن يُبَدِّلُواْ كَلَٰمَ ٱللَّهِۚ قُل لَّن تَتَّبِعُونَا كَذَٰلِكُمۡ قَالَ ٱللَّهُ مِن قَبۡلُۖ فَسَيَقُولُونَ بَلۡ تَحۡسُدُونَنَاۚ بَلۡ كَانُواْ لَا يَفۡقَهُونَ إِلَّا قَلِيلٗا ﴾
[الفَتح: 15]
﴿سيقول المخلفون إذا انطلقتم إلى مغانم لتأخذوها ذرونا نتبعكم يريدون أن يبدلوا﴾ [الفَتح: 15]
Abubakar Mahmood Jummi Waɗanda aka bari za su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganimomi* domin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bi ku." Suna son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Ba za ku bi mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabanin haka." Sa'an nan za su ce: "A'a, kuna dai hassadar mu ne." A'a, sun kasance ba su fahimtar (abubuwa) sai kaɗan |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗanda aka bari za su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganimomi domin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bi ku." Suna son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Ba za ku bi mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabanin haka." Sa'an nan za su ce: "A'a, kuna dai hassadar mu ne." A'a, sun kasance ba su fahimtar (abubuwa) sai kaɗan |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi dõmin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bĩ ku." Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka." Sa'an nan zã su ce: "Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne." Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai kaɗan |