Quran with Hausa translation - Surah Al-hujurat ayat 7 - الحُجُرَات - Page - Juz 26
﴿وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ فِيكُمۡ رَسُولَ ٱللَّهِۚ لَوۡ يُطِيعُكُمۡ فِي كَثِيرٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِ لَعَنِتُّمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ حَبَّبَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَزَيَّنَهُۥ فِي قُلُوبِكُمۡ وَكَرَّهَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡكُفۡرَ وَٱلۡفُسُوقَ وَٱلۡعِصۡيَانَۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلرَّٰشِدُونَ ﴾
[الحُجُرَات: 7]
﴿واعلموا أن فيكم رسول الله لو يطيعكم في كثير من الأمر لعنتم﴾ [الحُجُرَات: 7]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma ku sani (cewa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Da Yana bin ku ga (halaye) masu Yawa na al'amarin, da kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Ya soyar da imani a gare ku, kuma Ya ƙawata shi a cikin zukatanku kuma Ya ƙyamantar da kafirci da fasicci da saɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifofin nan) su ne shiryayyu |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma ku sani (cewa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Da Yana bin ku ga (halaye) masu Yawa na al'amarin, da kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Ya soyar da imani a gare ku, kuma Ya ƙawata shi a cikin zukatanku kuma Ya ƙyamantar da kafirci da fasicci da saɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifofin nan) su ne shiryayyu |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma ku sani (cẽwa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Dã Yana bin ku ga (hãlãye) mãsu Yawa na al'amarin, dã kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Yã sõyar da ĩmãni a gare ku, kuma Yã ƙawãta shi a cikin zukãtanku kuma Yã ƙyãmantar da kãfirci da fãsicci da sãɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifõfin nan) su ne shiryayyu |