×

A lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Ka tuna 5:110 Hausa translation

Quran infoHausaSurah Al-Ma’idah ⮕ (5:110) ayat 110 in Hausa

5:110 Surah Al-Ma’idah ayat 110 in Hausa (الهوسا)

Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 110 - المَائدة - Page - Juz 7

﴿إِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱذۡكُرۡ نِعۡمَتِي عَلَيۡكَ وَعَلَىٰ وَٰلِدَتِكَ إِذۡ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِ تُكَلِّمُ ٱلنَّاسَ فِي ٱلۡمَهۡدِ وَكَهۡلٗاۖ وَإِذۡ عَلَّمۡتُكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَۖ وَإِذۡ تَخۡلُقُ مِنَ ٱلطِّينِ كَهَيۡـَٔةِ ٱلطَّيۡرِ بِإِذۡنِي فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيۡرَۢا بِإِذۡنِيۖ وَتُبۡرِئُ ٱلۡأَكۡمَهَ وَٱلۡأَبۡرَصَ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡ تُخۡرِجُ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡ كَفَفۡتُ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ عَنكَ إِذۡ جِئۡتَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ ﴾
[المَائدة: 110]

A lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ¡udusi, kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩ Na, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã'ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai waɗanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne

❮ Previous Next ❯

ترجمة: إذ قال الله ياعيسى ابن مريم اذكر نعمتي عليك وعلى والدتك إذ, باللغة الهوسا

﴿إذ قال الله ياعيسى ابن مريم اذكر نعمتي عليك وعلى والدتك إذ﴾ [المَائدة: 110]

Abubakar Mahmood Jummi
A lokacin da Allah Ya ce: "Ya Isa ɗan Maryama! Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lokacin da Na ƙarfafa ka da Ruhul ¡udusi, kana yiwa mutane magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kana dattijo. Kuma a lokacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injila, kuma a lokacin da kake yin halitta daga laka kamar surar tsuntsu da iziniNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izini Na, kuma kana warkar da haifaffen makaho da kuturu, da iziniNa, kuma a lokacin da kake fitar da matattu da iziniNa, kuma a lokacin da Na kange Bani Isra'ila daga gare ka, a lokacin da ka je musu da hujjoji bayyanannu, sai waɗanda suka kafirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan ba kome ba ne, face sihiri bayyananne
Abubakar Mahmoud Gumi
A lokacin da Allah Ya ce: "Ya Isa ɗan Maryama! Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lokacin da Na ƙarfafa ka da Ruhul ¡udusi, kana yiwa mutane magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kana dattijo. Kuma a lokacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injila, kuma a lokacin da kake yin halitta daga laka kamar surar tsuntsu da iziniNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da iziniNa, kuma kana warkar da haifaffen makaho da kuturu, da iziniNa, kuma a lokacin da kake fitar da matattu da iziniNa, kuma a lokacin da Na kange Bani Isra'ila daga gare ka, a lokacin da ka je musu da hujjoji bayyanannu, sai waɗanda suka kafirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan ba kome ba ne, face sihiri bayyananne
Abubakar Mahmoud Gumi
A lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ¡udusi, kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã'ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai waɗanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne
❮ Previous Next ❯

Verse in more languages

Transliteration Bangla Bosnian German English Persian French Hindi Indonesian Kazakh Dutch Russian Spanish Turkish Urdu Uzbek