Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 44 - المَائدة - Page - Juz 6
﴿إِنَّآ أَنزَلۡنَا ٱلتَّوۡرَىٰةَ فِيهَا هُدٗى وَنُورٞۚ يَحۡكُمُ بِهَا ٱلنَّبِيُّونَ ٱلَّذِينَ أَسۡلَمُواْ لِلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلرَّبَّٰنِيُّونَ وَٱلۡأَحۡبَارُ بِمَا ٱسۡتُحۡفِظُواْ مِن كِتَٰبِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ عَلَيۡهِ شُهَدَآءَۚ فَلَا تَخۡشَوُاْ ٱلنَّاسَ وَٱخۡشَوۡنِ وَلَا تَشۡتَرُواْ بِـَٔايَٰتِي ثَمَنٗا قَلِيلٗاۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ ﴾
[المَائدة: 44]
﴿إنا أنـزلنا التوراة فيها هدى ونور يحكم بها النبيون الذين أسلموا للذين﴾ [المَائدة: 44]
Abubakar Mahmood Jummi Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabawa waɗanda suke sun sallama, suna yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da malaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littafin Allah, kuma sun kasance, a kansa, masu ba da shaida. To, kada ku ji tsoron mutane kuma ku ji tsoroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ayoyi Na. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai |
Abubakar Mahmoud Gumi Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabawa waɗanda suke sun sallama, suna yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da malaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littafin Allah, kuma sun kasance, a kansa, masu ba da shaida. To, kada ku ji tsoron mutane kuma ku ji tsoroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ayoyiNa. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai |
Abubakar Mahmoud Gumi Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabãwa waɗanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da mãlaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littãfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, mãsu bã da shaida. To, kada ku ji tsõron mutãne kuma ku ji tsõroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyoyiNa. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai |