Quran with Hausa translation - Surah Al-hadid ayat 10 - الحدِيد - Page - Juz 27
﴿وَمَا لَكُمۡ أَلَّا تُنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلِلَّهِ مِيرَٰثُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَا يَسۡتَوِي مِنكُم مَّنۡ أَنفَقَ مِن قَبۡلِ ٱلۡفَتۡحِ وَقَٰتَلَۚ أُوْلَٰٓئِكَ أَعۡظَمُ دَرَجَةٗ مِّنَ ٱلَّذِينَ أَنفَقُواْ مِنۢ بَعۡدُ وَقَٰتَلُواْۚ وَكُلّٗا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ ﴾
[الحدِيد: 10]
﴿وما لكم ألا تنفقوا في سبيل الله ولله ميراث السموات والأرض لا﴾ [الحدِيد: 10]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma me ya same ku, ba za ku ciyar ba domin ɗaukaka kalmar Allah, alhali kuwa gadon sammai da ƙasa na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabanin cin nasara, kuma ya yi yaƙi daga cikinku, ba ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafifita girman daraja* bisa ga waɗanda suka ciyar daga baya kuma suka yi yaƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma me ya same ku, ba za ku ciyar ba domin ɗaukaka kalmar Allah, alhali kuwa gadon sammai da ƙasa na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabanin cin nasara, kuma ya yi yaƙi daga cikinku, ba ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafifita girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga baya kuma suka yi yaƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafĩfĩta girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa |