Quran with Hausa translation - Surah Al-hashr ayat 7 - الحَشر - Page - Juz 28
﴿مَّآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰ فَلِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ كَيۡ لَا يَكُونَ دُولَةَۢ بَيۡنَ ٱلۡأَغۡنِيَآءِ مِنكُمۡۚ وَمَآ ءَاتَىٰكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَىٰكُمۡ عَنۡهُ فَٱنتَهُواْۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ ﴾
[الحَشر: 7]
﴿ما أفاء الله على رسوله من أهل القرى فلله وللرسول ولذي القربى﴾ [الحَشر: 7]
Abubakar Mahmood Jummi Abin da Allah Ya sanya shi ganima ga Manzon Sa dagamutanen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na Manzon Sa ne kuma na masu dangantaka da marayu da miskinai da ɗan hanya* (matafiyi) ne domin kada ya kasance abin shawagi a tsakanin mawadata daga cikinku kuma abin da Manzo ya ba ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙuba ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Abin da Allah Ya sanya shi ganima ga ManzonSa dagamutanen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na ManzonSa ne kuma na masu dangantaka da marayu da miskinai da ɗan hanya (matafiyi) ne domin kada ya kasance abin shawagi a tsakanin mawadata daga cikinku kuma abin da Manzo ya ba ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙuba ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga ManzonSa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na ManzonSa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya (matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne |