Quran with Hausa translation - Surah Al-Mumtahanah ayat 12 - المُمتَحنَة - Page - Juz 28
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ يُبَايِعۡنَكَ عَلَىٰٓ أَن لَّا يُشۡرِكۡنَ بِٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَلَا يَسۡرِقۡنَ وَلَا يَزۡنِينَ وَلَا يَقۡتُلۡنَ أَوۡلَٰدَهُنَّ وَلَا يَأۡتِينَ بِبُهۡتَٰنٖ يَفۡتَرِينَهُۥ بَيۡنَ أَيۡدِيهِنَّ وَأَرۡجُلِهِنَّ وَلَا يَعۡصِينَكَ فِي مَعۡرُوفٖ فَبَايِعۡهُنَّ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُنَّ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ ﴾
[المُمتَحنَة: 12]
﴿ياأيها النبي إذا جاءك المؤمنات يبايعنك على أن لا يشركن بالله شيئا﴾ [المُمتَحنَة: 12]
Abubakar Mahmood Jummi Ya kai Annabi! Idan mata muminai suka zo maka suna yi maka mubaya'a a kan ba za su yi shirki da Allah ba ga kome, kuma ba su yin sata, kuma ba su yin zina, kuma ba su kashe,* ya'yansu, kuma ba su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirawa** a tsakanin hannuwansu da ƙafafunsu kuma ba su saɓa maka ga wani abu da aka sani na shari'a, to, ka karɓi mubaya'arsu, kuma ka nemi Allah Ya gafarta musu. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya kai Annabi! Idan mata muminai suka zo maka suna yi maka mubaya'a a kan ba za su yi shirki da Allah ba ga kome, kuma ba su yin sata, kuma ba su yin zina, kuma ba su kashe, ya'yansu, kuma ba su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirawa a tsakanin hannuwansu da ƙafafunsu kuma ba su saɓa maka ga wani abu da aka sani na shari'a, to, ka karɓi mubaya'arsu, kuma ka nemi Allah Ya gafarta musu. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã kai Annabi! Idan mãtã mũminai suka zo maka sunã yi maka mubãya'a a kan bã zã su yi shirki da Allah ba ga kõme, kuma bã su yin sãtã, kuma bã su yin zina, kuma bã su kashe, ya'yansu, kuma bã su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirãwa a tsãkanin hannuwansu da ƙafãfunsu kuma bã su sãɓa maka ga wani abu da aka sani na sharĩ'a, to, ka karɓi mubãya'arsu, kuma ka nẽmi Allah Ya gãfarta musu. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai |