Quran with Hausa translation - Surah Al-A‘raf ayat 146 - الأعرَاف - Page - Juz 9
﴿سَأَصۡرِفُ عَنۡ ءَايَٰتِيَ ٱلَّذِينَ يَتَكَبَّرُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَإِن يَرَوۡاْ كُلَّ ءَايَةٖ لَّا يُؤۡمِنُواْ بِهَا وَإِن يَرَوۡاْ سَبِيلَ ٱلرُّشۡدِ لَا يَتَّخِذُوهُ سَبِيلٗا وَإِن يَرَوۡاْ سَبِيلَ ٱلۡغَيِّ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلٗاۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ عَنۡهَا غَٰفِلِينَ ﴾
[الأعرَاف: 146]
﴿سأصرف عن آياتي الذين يتكبرون في الأرض بغير الحق وإن يروا كل﴾ [الأعرَاف: 146]
Abubakar Mahmood Jummi Za Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, ba da wani hakki ba, daga ayoyiNa. Kuma idan sun ga dukan aya, ba za su yi imani da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, ba za su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, domin lalle ne su, sun ƙaryata da ayoyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gafilai |
Abubakar Mahmoud Gumi Za Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, ba da wani hakki ba, daga ayoyiNa. Kuma idan sun ga dukan aya, ba za su yi imani da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, ba za su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, domin lalle ne su, sun ƙaryata da ayoyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gafilai |
Abubakar Mahmoud Gumi Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai |