Quran with Hausa translation - Surah Hud ayat 31 - هُود - Page - Juz 12
﴿وَلَآ أَقُولُ لَكُمۡ عِندِي خَزَآئِنُ ٱللَّهِ وَلَآ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ وَلَآ أَقُولُ إِنِّي مَلَكٞ وَلَآ أَقُولُ لِلَّذِينَ تَزۡدَرِيٓ أَعۡيُنُكُمۡ لَن يُؤۡتِيَهُمُ ٱللَّهُ خَيۡرًاۖ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا فِيٓ أَنفُسِهِمۡ إِنِّيٓ إِذٗا لَّمِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴾
[هُود: 31]
﴿ولا أقول لكم عندي خزائن الله ولا أعلم الغيب ولا أقول إني﴾ [هُود: 31]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma ba ni ce muku a wurina taskokin Allah suke kuma ba ina sanin gaibi ba ne. Kuma ba ina cewa ni Mala'ika ba ne. Kuma ba ni cewa ga waɗanda idanunku suke wulakantawa, Allah ba zai ba su alheri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (na yi haka) da ina daga cikin azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma ba ni ce muku a wurina taskokin Allah suke kuma ba ina sanin gaibi ba ne. Kuma ba ina cewa ni Mala'ika ba ne. Kuma ba ni cewa ga waɗanda idanunku suke wulakantawa, Allah ba zai ba su alheri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (na yi haka) da ina daga cikin azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma bã ni ce muku a wurĩna taskõkin Allah suke kuma bã inã sanin gaibi ba ne. Kuma ba inã cẽwa ni Malã'ika ba ne. Kuma ba ni cẽwa ga waɗanda idãnunku suke wulãkantãwa, Allah bã zai bã su alhẽri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (nã yi haka) dã ina daga cikin azzalumai |