Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 133 - البَقَرَة - Page - Juz 1
﴿أَمۡ كُنتُمۡ شُهَدَآءَ إِذۡ حَضَرَ يَعۡقُوبَ ٱلۡمَوۡتُ إِذۡ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعۡبُدُونَ مِنۢ بَعۡدِيۖ قَالُواْ نَعۡبُدُ إِلَٰهَكَ وَإِلَٰهَ ءَابَآئِكَ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ إِلَٰهٗا وَٰحِدٗا وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ ﴾
[البَقَرَة: 133]
﴿أم كنتم شهداء إذ حضر يعقوب الموت إذ قال لبنيه ما تعبدون﴾ [البَقَرَة: 133]
Abubakar Mahmood Jummi Ko kun* kasance halarce a lokacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙubu, a lokacin da ya ce wa ɗiyansa: "Mene ne za ku bauta wa daga bayana?" Suka ce: "Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrahim da lsma'ila da Is'haƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi masu miƙa wuya ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Ko kun kasance halarce a lokacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙubu, a lokacin da ya ce wa ɗiyansa: "Mene ne za ku bauta wa daga bayana?" Suka ce: "Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrahim da lsma'ila da Is'haƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi masu miƙa wuya ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Ko kun kasance halarce a lõkacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙũbu, a lõkacin da ya ce wa ɗiyansa: "Mẽne ne zã ku bauta wa daga bãyãna?" Suka ce: "Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrãhĩm da lsmã'ĩla da Is'hãƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi mãsu miƙa wuya ne |