Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 150 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿وَمِنۡ حَيۡثُ خَرَجۡتَ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَحَيۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُۥ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَيۡكُمۡ حُجَّةٌ إِلَّا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡهُمۡ فَلَا تَخۡشَوۡهُمۡ وَٱخۡشَوۡنِي وَلِأُتِمَّ نِعۡمَتِي عَلَيۡكُمۡ وَلَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ ﴾
[البَقَرَة: 150]
﴿ومن حيث خرجت فول وجهك شطر المسجد الحرام وحيث ما كنتم فولوا﴾ [البَقَرَة: 150]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma daga inda ka fita, to, ka juyar da fuskarka a wajen Masallaci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku juyar da fuskokinku a wajensa, domin kada wata hujja ta kasance ga mutane a kanku, face waɗanda suka yi zalunci daga gare su. Saboda haka kada ku ji tsoronsu kuma ku ji tsoroNa kuma domin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammaninku za ku shiryu |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma daga inda ka fita, to, ka juyar da fuskarka a wajen Masallaci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku juyar da fuskokinku a wajensa, domin kada wata hujja ta kasance ga mutane a kanku, face waɗanda suka yi zalunci daga gare su. Saboda haka kada ku ji tsoronsu kuma ku ji tsoroNa kuma domin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammaninku za ku shiryu |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma daga inda ka fita, to, ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku jũyar da fuskõkinku a wajensa, dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kanku, fãce waɗanda suka yi zãlunci daga gare su. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõrõNa kuma dõmin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammãninku zã ku shiryu |