Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 246 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ مِنۢ بَعۡدِ مُوسَىٰٓ إِذۡ قَالُواْ لِنَبِيّٖ لَّهُمُ ٱبۡعَثۡ لَنَا مَلِكٗا نُّقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ قَالَ هَلۡ عَسَيۡتُمۡ إِن كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِتَالُ أَلَّا تُقَٰتِلُواْۖ قَالُواْ وَمَا لَنَآ أَلَّا نُقَٰتِلَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَقَدۡ أُخۡرِجۡنَا مِن دِيَٰرِنَا وَأَبۡنَآئِنَاۖ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقِتَالُ تَوَلَّوۡاْ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّٰلِمِينَ ﴾
[البَقَرَة: 246]
﴿ألم تر إلى الملإ من بني إسرائيل من بعد موسى إذ قالوا﴾ [البَقَرَة: 246]
Abubakar Mahmood Jummi Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashawarta* daga Bani Isra'ila daga bayan Musa, a lokacinda suka ce ga wani annabi nasu: "Naɗa mana sarki, mu yi yaƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammaninku idan an wajabta yaƙi a kanku cewa ba za ku yi yaƙin ba?" Suka ce: "Kuma mene ne a gare mu, ba za mu yi yaƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhali kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidajenmu da ɗiyanmu?" To, a lokacin da aka wajabta yaƙin a kansu, suka juya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashawarta daga Bani Isra'ila daga bayan Musa, a lokacinda suka ce ga wani annabi nasu: "Naɗa mana sarki, mu yi yaƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammaninku idan an wajabta yaƙi a kanku cewa ba za ku yi yaƙin ba?" Suka ce: "Kuma mene ne a gare mu, ba za mu yi yaƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhali kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidajenmu da ɗiyanmu?" To, a lokacin da aka wajabta yaƙin a kansu, suka juya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacinda suka ce ga wani annabi nãsu: "Naɗã mana sarki, mu yi yãƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammãninku idan an wajabta yãƙi a kanku cẽwa bã zã ku yi yãƙin ba?" Suka ce: "Kuma mẽne ne a gare mu, ba zã mu yi yãƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidãjenmu da ɗiyanmu?" To, a lõkacin da aka wajabta yãƙin a kansu, suka jũya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai |