Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 255 - البَقَرَة - Page - Juz 3
﴿ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ ﴾
[البَقَرَة: 255]
﴿الله لا إله إلا هو الحي القيوم لا تأخذه سنة ولا نوم﴾ [البَقَرَة: 255]
Abubakar Mahmood Jummi Allah, babu wani Ubangiji face Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da kome, gyangyaɗi ba ya kama Shi, kuma barci ba ya kama Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin ceto a wurinSa, face da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bayansu. Kuma ba su kewayewa da kome daga ilminSa, face da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su ba ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma |
Abubakar Mahmoud Gumi Allah, babu wani Ubangiji face Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da kome, gyangyaɗi ba ya kama Shi, kuma barci ba ya kama Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin ceto a wurinSa, face da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bayansu. Kuma ba su kewayewa da kome daga ilminSa, face da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su ba ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma |
Abubakar Mahmoud Gumi Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma |