Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 258 - البَقَرَة - Page - Juz 3
﴿أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِي حَآجَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ فِي رَبِّهِۦٓ أَنۡ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ إِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّيَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ قَالَ أَنَا۠ أُحۡيِۦ وَأُمِيتُۖ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَأۡتِي بِٱلشَّمۡسِ مِنَ ٱلۡمَشۡرِقِ فَأۡتِ بِهَا مِنَ ٱلۡمَغۡرِبِ فَبُهِتَ ٱلَّذِي كَفَرَۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴾
[البَقَرَة: 258]
﴿ألم تر إلى الذي حاج إبراهيم في ربه أن آتاه الله الملك﴾ [البَقَرَة: 258]
Abubakar Mahmood Jummi Shin, ba ka gani* ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrahim a cikin (al'amarin) Ubangijinsa domin Allah Ya ba shi mulki, a lokacin da Ibrahim ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rayawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Ni ina rayarwa kuma ina matarwa." Ibrahim ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakafirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrahim a cikin (al'amarin) Ubangijinsa domin Allah Ya ba shi mulki, a lokacin da Ibrahim ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rayawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Ni ina rayarwa kuma ina matarwa." Ibrahim ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakafirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai |