Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 259 - البَقَرَة - Page - Juz 3
﴿أَوۡ كَٱلَّذِي مَرَّ عَلَىٰ قَرۡيَةٖ وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّىٰ يُحۡيِۦ هَٰذِهِ ٱللَّهُ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۖ فَأَمَاتَهُ ٱللَّهُ مِاْئَةَ عَامٖ ثُمَّ بَعَثَهُۥۖ قَالَ كَمۡ لَبِثۡتَۖ قَالَ لَبِثۡتُ يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖۖ قَالَ بَل لَّبِثۡتَ مِاْئَةَ عَامٖ فَٱنظُرۡ إِلَىٰ طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمۡ يَتَسَنَّهۡۖ وَٱنظُرۡ إِلَىٰ حِمَارِكَ وَلِنَجۡعَلَكَ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِۖ وَٱنظُرۡ إِلَى ٱلۡعِظَامِ كَيۡفَ نُنشِزُهَا ثُمَّ نَكۡسُوهَا لَحۡمٗاۚ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥ قَالَ أَعۡلَمُ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ ﴾
[البَقَرَة: 259]
﴿أو كالذي مر على قرية وهي خاوية على عروشها قال أنى يحيي﴾ [البَقَرَة: 259]
Abubakar Mahmood Jummi Ko kuwa* wanda ya shuɗe a kan wata alƙarya, alhali kuwa tana wofintacciya a kan gadajen resunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rayar da wannan a bayan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shekara ɗari; sa'an nankuma ya tayar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a ka zauna shekara ɗari." To, ka duba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kowanensu) bai sake ba, kuma ka duba zuwa ga jakinka, kuma domin Mu sanya ka wata aya ga mutane. Kuma ka duba zuwa ga ƙasusuwa yadda Muke motsarda su sa'an nan kuma Mu tufatar da su, da nama", To, a lokacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cewa lalle Allah a kan dukan kome Mai ikon yi ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Ko kuwa wanda ya shuɗe a kan wata alƙarya, alhali kuwa tana wofintacciya a kan gadajen resunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rayar da wannan a bayan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shekara ɗari; sa'an nankuma ya tayar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a ka zauna shekara ɗari." To, ka duba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kowanensu) bai sake ba, kuma ka duba zuwa ga jakinka, kuma domin Mu sanya ka wata aya ga mutane. Kuma ka duba zuwa ga ƙasusuwa yadda Muke motsarda su sa'an nan kuma Mu tufatar da su, da nama", To, a lokacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cewa lalle Allah a kan dukan kome Mai ikon yi ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kõ kuwa wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne |