Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 267 - البَقَرَة - Page - Juz 3
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنفِقُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا كَسَبۡتُمۡ وَمِمَّآ أَخۡرَجۡنَا لَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِۖ وَلَا تَيَمَّمُواْ ٱلۡخَبِيثَ مِنۡهُ تُنفِقُونَ وَلَسۡتُم بِـَٔاخِذِيهِ إِلَّآ أَن تُغۡمِضُواْ فِيهِۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٌ ﴾
[البَقَرَة: 267]
﴿ياأيها الذين آمنوا أنفقوا من طيبات ما كسبتم ومما أخرجنا لكم من﴾ [البَقَرَة: 267]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗan da suka yi imani! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sana'anta, kuma daga abin da Muka fitar saboda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhali kuwa ba ku zama masu karɓarsa ba face kun runtse ido a cikin sa. Kuma ku sani cewa lalle ne, Allah Mawadaci ne, Godadde |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sana'anta, kuma daga abin da Muka fitar saboda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhali kuwa ba ku zama masu karɓarsa ba face kun runtse ido a cikinsa. Kuma ku sani cewa lalle ne, Allah Mawadaci ne, Godadde |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sanã'anta, kuma daga abin da Muka fitar sabõda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhãli kuwa ba ku zama mãsu karɓarsa ba fãce kun runtse ido a cikinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mawadãci ne, Gõdadde |