Quran with Hausa translation - Surah al-‘Imran ayat 152 - آل عِمران - Page - Juz 4
﴿وَلَقَدۡ صَدَقَكُمُ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥٓ إِذۡ تَحُسُّونَهُم بِإِذۡنِهِۦۖ حَتَّىٰٓ إِذَا فَشِلۡتُمۡ وَتَنَٰزَعۡتُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِ وَعَصَيۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ مَآ أَرَىٰكُم مَّا تُحِبُّونَۚ مِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلدُّنۡيَا وَمِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلۡأٓخِرَةَۚ ثُمَّ صَرَفَكُمۡ عَنۡهُمۡ لِيَبۡتَلِيَكُمۡۖ وَلَقَدۡ عَفَا عَنكُمۡۗ وَٱللَّهُ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ﴾
[آل عِمران: 152]
﴿ولقد صدقكم الله وعده إذ تحسونهم بإذنه حتى إذا فشلتم وتنازعتم في﴾ [آل عِمران: 152]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma lalle ne haƙiƙa Allah Ya yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lokacin da kuka kasa,* kuma kuka yi jayayya a cikin al'amarin, kuma kuka saɓa a bayan (Allah) Ya nuna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lahira. Sa'an nan kuma Ya juyar da ku daga gare su, domin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙiƙa, Ya yafe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga muminai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma lalle ne haƙiƙa Allah Ya yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lokacin da kuka kasa, kuma kuka yi jayayya a cikin al'amarin, kuma kuka saɓa a bayan (Allah) Ya nuna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lahira. Sa'an nan kuma Ya juyar da ku daga gare su, domin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙiƙa, Ya yafe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga muminai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lõkacin da kuka kãsa, kuma kuka yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma kuka sãɓã a bãyan (Allah) Ya nũna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lãhĩra. Sa'an nan kuma Ya jũyar da ku daga gare su, dõmin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Ya yãfe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga mũminai |