Quran with Hausa translation - Surah An-Nisa’ ayat 3 - النِّسَاء - Page - Juz 4
﴿وَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا تُقۡسِطُواْ فِي ٱلۡيَتَٰمَىٰ فَٱنكِحُواْ مَا طَابَ لَكُم مِّنَ ٱلنِّسَآءِ مَثۡنَىٰ وَثُلَٰثَ وَرُبَٰعَۖ فَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا تَعۡدِلُواْ فَوَٰحِدَةً أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَلَّا تَعُولُواْ ﴾
[النِّسَاء: 3]
﴿وإن خفتم ألا تقسطوا في اليتامى فانكحوا ما طاب لكم من النساء﴾ [النِّسَاء: 3]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba a cikin marayu,* to, (akwai yadda za a yi) ku auri abin da ya yi muku daɗi daga mata; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba a cikin marayu, to, (akwai yadda za a yi) ku auri abin da ya yi muku daɗi daga mata; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, to, (akwai yadda zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba |