Quran with Hausa translation - Surah Al-hujurat ayat 11 - الحُجُرَات - Page - Juz 26
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَسۡخَرۡ قَوۡمٞ مِّن قَوۡمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُواْ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا نِسَآءٞ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيۡرٗا مِّنۡهُنَّۖ وَلَا تَلۡمِزُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَلَا تَنَابَزُواْ بِٱلۡأَلۡقَٰبِۖ بِئۡسَ ٱلِٱسۡمُ ٱلۡفُسُوقُ بَعۡدَ ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن لَّمۡ يَتُبۡ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ ﴾
[الحُجُرَات: 11]
﴿ياأيها الذين آمنوا لا يسخر قوم من قوم عسى أن يكونوا خيرا﴾ [الحُجُرَات: 11]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada waɗansu mutane su yi izgili game da waɗansu mutane, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma waɗansu mata kada su yi izgili game da waɗansu mata mai yiwuwa ne su kasancc mafifita daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na laƙabobi. Tir da suna na fasicci a bayan imani. Kuma wanda bai tuba ba, to, waɗannan su ne azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada waɗansu mutane su yi izgili game da waɗansu mutane, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma waɗansu mata kada su yi izgili game da waɗansu mata mai yiwuwa ne su kasancc mafifita daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na laƙabobi. Tir da suna na fasicci a bayan imani. Kuma wanda bai tuba ba, to, waɗannan su ne azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai |