Quran with Hausa translation - Surah Al-An‘am ayat 158 - الأنعَام - Page - Juz 8
﴿هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن تَأۡتِيَهُمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ أَوۡ يَأۡتِيَ رَبُّكَ أَوۡ يَأۡتِيَ بَعۡضُ ءَايَٰتِ رَبِّكَۗ يَوۡمَ يَأۡتِي بَعۡضُ ءَايَٰتِ رَبِّكَ لَا يَنفَعُ نَفۡسًا إِيمَٰنُهَا لَمۡ تَكُنۡ ءَامَنَتۡ مِن قَبۡلُ أَوۡ كَسَبَتۡ فِيٓ إِيمَٰنِهَا خَيۡرٗاۗ قُلِ ٱنتَظِرُوٓاْ إِنَّا مُنتَظِرُونَ ﴾
[الأنعَام: 158]
﴿هل ينظرون إلا أن تأتيهم الملائكة أو يأتي ربك أو يأتي بعض﴾ [الأنعَام: 158]
Abubakar Mahmood Jummi Shin, suna jiran (wani abu), face dai mala'iku* su je musu ko kuwa Ubangijinka Ya je, ko kuwa sashen ayoyin Ubangijinka ya je. A ranar da sashen ayoyin Ubangijinka yake zuwa, imanin rai wanda bai kasance ya yi imanin ba a gabani, ko kuwa ya yi tsiwirwirin wani alheri, ba ya amfaninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mu, masu jira ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Shin, suna jiran (wani abu), face dai mala'iku su je musu ko kuwa Ubangijinka Ya je, ko kuwa sashen ayoyin Ubangijinka ya je. A ranar da sashen ayoyin Ubangijinka yake zuwa, imanin rai wanda bai kasance ya yi imanin ba a gabani, ko kuwa ya yi tsiwirwirin wani alheri, ba ya amfaninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mu, masu jira ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Shin, sunã jiran (wani abu), fãce dai malã'iku su je musu kõ kuwa Ubangijinka Ya je, kõ kuwa sãshen ãyõyin Ubangijinka ya je. A rãnar da sãshen ãyõyin Ubangijinka yake zuwa, ĩmãnin rai wanda bai kasance yã yi ĩmãnin ba a gabãni, kõ kuwa ya yi tsiwirwirin wani alhẽri, bã ya amfãninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mũ, mãsu jira ne |