Quran with Hausa translation - Surah Al-An‘am ayat 59 - الأنعَام - Page - Juz 7
﴿۞ وَعِندَهُۥ مَفَاتِحُ ٱلۡغَيۡبِ لَا يَعۡلَمُهَآ إِلَّا هُوَۚ وَيَعۡلَمُ مَا فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِۚ وَمَا تَسۡقُطُ مِن وَرَقَةٍ إِلَّا يَعۡلَمُهَا وَلَا حَبَّةٖ فِي ظُلُمَٰتِ ٱلۡأَرۡضِ وَلَا رَطۡبٖ وَلَا يَابِسٍ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٖ ﴾
[الأنعَام: 59]
﴿وعنده مفاتح الغيب لا يعلمها إلا هو ويعلم ما في البر والبحر﴾ [الأنعَام: 59]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma a wurin Sa mabudan* gaibi suke, babu wanda yake sanin su face Shi, kuma Yana sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya faɗuwa, face Ya san shi, kuma babu wata ƙwaya a cikin duffan ƙasa, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙeƙasasshe, face yana a cikin wani Littafi mai bayyanawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma a wurinSa mabudan gaibi suke, babu wanda yake sanin su face Shi, kuma Yana sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya faɗuwa, face Ya san shi, kuma babu wata ƙwaya a cikin duffan ƙasa, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙeƙasasshe, face yana a cikin wani Littafi mai bayyanawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma a wurinSa mabũdan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa |