Quran with Hausa translation - Surah Al-An‘am ayat 71 - الأنعَام - Page - Juz 7
﴿قُلۡ أَنَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُنَا وَلَا يَضُرُّنَا وَنُرَدُّ عَلَىٰٓ أَعۡقَابِنَا بَعۡدَ إِذۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُ كَٱلَّذِي ٱسۡتَهۡوَتۡهُ ٱلشَّيَٰطِينُ فِي ٱلۡأَرۡضِ حَيۡرَانَ لَهُۥٓ أَصۡحَٰبٞ يَدۡعُونَهُۥٓ إِلَى ٱلۡهُدَى ٱئۡتِنَاۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۖ وَأُمِرۡنَا لِنُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴾
[الأنعَام: 71]
﴿قل أندعوا من دون الله ما لا ينفعنا ولا يضرنا ونرد على﴾ [الأنعَام: 71]
Abubakar Mahmood Jummi Ka ce: "Shin, za mu yi kiran abin da ba ya amfaninmu, baicin Allah, kuma ba ya cutar damu, kuma a mayar da mu a kan dugaduganmu, a bayan Allah Ya shiryar da mu kamar wanda shaiɗanu suka kayar da shi a cikin ƙasa, yana mai ɗimuwa, yana da abokaisuna kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'"* Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin talikai |
Abubakar Mahmoud Gumi Ka ce: "Shin, za mu yi kiran abin da ba ya amfaninmu, baicin Allah, kuma ba ya cutar damu, kuma a mayar da mu a kan dugaduganmu, a bayan Allah Ya shiryar da mu kamar wanda shaiɗanu suka kayar da shi a cikin ƙasa, yana mai ɗimuwa, yana da abokaisuna kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'" Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin talikai |
Abubakar Mahmoud Gumi Ka ce: "Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'" Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai |