Quran with Hausa translation - Surah Al-Mumtahanah ayat 1 - المُمتَحنَة - Page - Juz 28
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ عَدُوِّي وَعَدُوَّكُمۡ أَوۡلِيَآءَ تُلۡقُونَ إِلَيۡهِم بِٱلۡمَوَدَّةِ وَقَدۡ كَفَرُواْ بِمَا جَآءَكُم مِّنَ ٱلۡحَقِّ يُخۡرِجُونَ ٱلرَّسُولَ وَإِيَّاكُمۡ أَن تُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ رَبِّكُمۡ إِن كُنتُمۡ خَرَجۡتُمۡ جِهَٰدٗا فِي سَبِيلِي وَٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِيۚ تُسِرُّونَ إِلَيۡهِم بِٱلۡمَوَدَّةِ وَأَنَا۠ أَعۡلَمُ بِمَآ أَخۡفَيۡتُمۡ وَمَآ أَعۡلَنتُمۡۚ وَمَن يَفۡعَلۡهُ مِنكُمۡ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ ﴾
[المُمتَحنَة: 1]
﴿ياأيها الذين آمنوا لا تتخذوا عدوي وعدوكم أولياء تلقون إليهم بالمودة وقد﴾ [المُمتَحنَة: 1]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi maƙiyi Na kuma maƙiyinku masoyi, . Kuna jefa soyayya* zuwa gare su, alhali kuwa haƙiƙa sun kafirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, suna fitar da Manzon Allah tare da ku (daga gidajenku) domin kun yi imani da Allah, Ubangijinku, idan kun fito domin jihadi saboda ɗaukaka kalmaTa da neman yardaTa, kuna asirta soyayya zuwa gare su alhali kuwa Ni ne Mafi sani ga abin da kuka ɓoye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi maƙiyiNa kuma maƙiyinku masoyi, 845. Kuna jefa soyayya zuwa gare su, alhali kuwa haƙiƙa sun kafirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, suna fitar da Manzon Allah tare da ku (daga gidajenku) domin kun yi imani da Allah, Ubangijinku, idan kun fito domin jihadi saboda ɗaukaka kalmaTa da neman yardaTa, kuna asirta soyayya zuwa gare su alhali kuwa Ni ne Mafi sani ga abin da kuka ɓoye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩNa kuma maƙiyinku masõyi, 845. Kuna jẽfa sõyayya zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku (daga gidãjenku) dõmin kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya |