Quran with Hausa translation - Surah AT-Talaq ayat 6 - الطَّلَاق - Page - Juz 28
﴿أَسۡكِنُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ سَكَنتُم مِّن وُجۡدِكُمۡ وَلَا تُضَآرُّوهُنَّ لِتُضَيِّقُواْ عَلَيۡهِنَّۚ وَإِن كُنَّ أُوْلَٰتِ حَمۡلٖ فَأَنفِقُواْ عَلَيۡهِنَّ حَتَّىٰ يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ فَإِنۡ أَرۡضَعۡنَ لَكُمۡ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ وَأۡتَمِرُواْ بَيۡنَكُم بِمَعۡرُوفٖۖ وَإِن تَعَاسَرۡتُمۡ فَسَتُرۡضِعُ لَهُۥٓ أُخۡرَىٰ ﴾
[الطَّلَاق: 6]
﴿أسكنوهن من حيث سكنتم من وجدكم ولا تضاروهن لتضيقوا عليهن وإن كن﴾ [الطَّلَاق: 6]
Abubakar Mahmood Jummi Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar* daga gwargwadon samunku. Kuma kada ku cuce su domin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abuta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shayar da mama saboda ku, sai ku ba su tsadodinsu. Kuma ku yi shawara a tsakaninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nuna talauci to wata mace za ta shayar da mama saboda shi (mijin) |
Abubakar Mahmoud Gumi Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar daga gwargwadon samunku. Kuma kada ku cuce su domin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abuta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shayar da mama saboda ku, sai ku ba su tsadodinsu. Kuma ku yi shawara a tsakaninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nuna talauci to wata mace za ta shayar da mama saboda shi (mijin) |
Abubakar Mahmoud Gumi Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar daga gwargwadon sãmunku. Kuma kada ku cũce su dõmin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abũta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shãyar da mãma sabõda ku, sai ku bã su tsãdõdinsu. Kuma ku yi shãwara a tsakãninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nũna talauci to wata mace zã ta shãyar da mãma sabõda shi (mijin) |