Quran with Hausa translation - Surah At-Taubah ayat 28 - التوبَة - Page - Juz 10
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡمُشۡرِكُونَ نَجَسٞ فَلَا يَقۡرَبُواْ ٱلۡمَسۡجِدَ ٱلۡحَرَامَ بَعۡدَ عَامِهِمۡ هَٰذَاۚ وَإِنۡ خِفۡتُمۡ عَيۡلَةٗ فَسَوۡفَ يُغۡنِيكُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦٓ إِن شَآءَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ حَكِيمٞ ﴾
[التوبَة: 28]
﴿ياأيها الذين آمنوا إنما المشركون نجس فلا يقربوا المسجد الحرام بعد عامهم﴾ [التوبَة: 28]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, saboda haka kada su kusanci Masallaci Mai Alfarma a bayan shekarar su wannan. Kuma idan kun ji tsoron talauci* to, da sannu Allah zai wadata ku daga falalar Sa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, saboda haka kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bayan shekararsu wannan. Kuma idan kun ji tsoron talauci to, da sannu Allah zai wadata ku daga falalarSa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bãyan shẽkararsu wannan. Kuma idan kun ji tsõron talauci to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalarSa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima |