Quran with Hausa translation - Surah At-Taubah ayat 34 - التوبَة - Page - Juz 10
﴿۞ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡأَحۡبَارِ وَٱلرُّهۡبَانِ لَيَأۡكُلُونَ أَمۡوَٰلَ ٱلنَّاسِ بِٱلۡبَٰطِلِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۗ وَٱلَّذِينَ يَكۡنِزُونَ ٱلذَّهَبَ وَٱلۡفِضَّةَ وَلَا يُنفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٖ ﴾
[التوبَة: 34]
﴿ياأيها الذين آمنوا إن كثيرا من الأحبار والرهبان ليأكلون أموال الناس بالباطل﴾ [التوبَة: 34]
Abubakar Mahmood Jummi Ya waɗanda suka yi imani! Lalle ne masu yawa daga Ahbar* da Ruhbanawa haƙiƙa suna cin dukiyar mutane da ƙarya, kuma suna kangewa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacewar zinariya da azurfa, kuma ba su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushara da azaba mai raɗaɗi |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya waɗanda suka yi imani! Lalle ne masu yawa daga Ahbar da Ruhbanawa haƙiƙa suna cin dukiyar mutane da ƙarya, kuma suna kangewa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacewar zinariya da azurfa, kuma ba su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushara da azaba mai raɗaɗi |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi |