Quran with Hausa translation - Surah Al-Kahf ayat 31 - الكَهف - Page - Juz 15
﴿أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ جَنَّٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَيَلۡبَسُونَ ثِيَابًا خُضۡرٗا مِّن سُندُسٖ وَإِسۡتَبۡرَقٖ مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِۚ نِعۡمَ ٱلثَّوَابُ وَحَسُنَتۡ مُرۡتَفَقٗا ﴾
[الكَهف: 31]
﴿أولئك لهم جنات عدن تجري من تحتهم الأنهار يحلون فيها من أساور﴾ [الكَهف: 31]
Abubakar Mahmood Jummi Waɗannan suna da gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, ana sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundaye na zinariya, kuma suna tufantar waɗansu tufafi kore, na alharini raƙiƙi da alharini mai kauri suna kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu. Madalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗannan suna da gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, ana sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundaye na zinariya, kuma suna tufantar waɗansu tufafi kore, na alharini raƙiƙi da alharini mai kauri suna kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu. Madalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Waɗannan sunã da gidãjen Aljannar zama, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, anã sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar waɗansu tũfãfi kõre, na alharĩni raƙĩƙi da alharini mai kauri sunã kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa |