Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 251 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿فَهَزَمُوهُم بِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَقَتَلَ دَاوُۥدُ جَالُوتَ وَءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَهُۥ مِمَّا يَشَآءُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّفَسَدَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴾
[البَقَرَة: 251]
﴿فهزموهم بإذن الله وقتل داود جالوت وآتاه الله الملك والحكمة وعلمه مما﴾ [البَقَرَة: 251]
Abubakar Mahmood Jummi Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dawudu ya kashe Jaluta, kuma Allah Ya ba shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma ba domin tunkuɗewar Allah ga mutane sashensu da sashe ba lalle ne da ƙasa ta ɓaci; kuma amma Allah Ma'abucin falala ne a kan talikai |
Abubakar Mahmoud Gumi Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dawudu ya kashe Jaluta, kuma Allah Ya ba shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma ba domin tunkuɗewar Allah ga mutane sashensu da sashe ba lalle ne da ƙasa ta ɓaci; kuma amma Allah Ma'abucin falala ne a kan talikai |
Abubakar Mahmoud Gumi Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dãwudu ya kashe Jãlũta, kuma Allah Ya bã shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma bã dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne sãshensu da sãshe ba lalle ne dã ƙasa tã ɓãci; kuma amma Allah Ma'abũcin falala ne a kan tãlikai |