Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 61 - البَقَرَة - Page - Juz 1
﴿وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نَّصۡبِرَ عَلَىٰ طَعَامٖ وَٰحِدٖ فَٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُخۡرِجۡ لَنَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۢ بَقۡلِهَا وَقِثَّآئِهَا وَفُومِهَا وَعَدَسِهَا وَبَصَلِهَاۖ قَالَ أَتَسۡتَبۡدِلُونَ ٱلَّذِي هُوَ أَدۡنَىٰ بِٱلَّذِي هُوَ خَيۡرٌۚ ٱهۡبِطُواْ مِصۡرٗا فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلۡتُمۡۗ وَضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلذِّلَّةُ وَٱلۡمَسۡكَنَةُ وَبَآءُو بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ ﴾
[البَقَرَة: 61]
﴿وإذ قلتم ياموسى لن نصبر على طعام واحد فادع لنا ربك يخرج﴾ [البَقَرَة: 61]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma a lokacin da kuka ce: "Ya Musa! Ba za mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka roƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna neman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alheri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka roƙa. "Kuma Muka doka musu walaƙanci da talauci. Kuma suka koma da wani fushi daga Allah. Wancan saboda lalle su, sun kasance suna kafirta da ayoyin Allah, kuma suna kashe Aannabawa, bada hakki ba. Wancan, saboda saɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙetarewar haddi |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma a lokacin da kuka ce: "Ya Musa! Ba za mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka roƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna neman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alheri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka roƙa. "Kuma Muka doka musu walaƙanci da talauci. Kuma suka koma da wani fushi daga Allah. Wancan saboda lalle su, sun kasance suna kafirta da ayoyin Allah, kuma suna kashe Aannabawa, bada hakki ba. Wancan, saboda saɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙetarewar haddi |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma a lõkacin da kuka ce: "Yã Mũsã! Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna nẽman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. "Kuma Muka dõka musu walãƙanci da talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Aannabãwa, bãda hakki ba. Wancan, sabõda sãɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi |