Quran with Hausa translation - Surah An-Naml ayat 40 - النَّمل - Page - Juz 19
﴿قَالَ ٱلَّذِي عِندَهُۥ عِلۡمٞ مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن يَرۡتَدَّ إِلَيۡكَ طَرۡفُكَۚ فَلَمَّا رَءَاهُ مُسۡتَقِرًّا عِندَهُۥ قَالَ هَٰذَا مِن فَضۡلِ رَبِّي لِيَبۡلُوَنِيٓ ءَأَشۡكُرُ أَمۡ أَكۡفُرُۖ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيّٞ كَرِيمٞ ﴾
[النَّمل: 40]
﴿قال الذي عنده علم من الكتاب أنا آتيك به قبل أن يرتد﴾ [النَّمل: 40]
Abubakar Mahmood Jummi Wanda yake a wurinsa akwai* wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni ina zo maka da shi a gabanin ƙyaftawar ganinka ta koma gare ka." To, a lokacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijina yake, domin Ya jarraba ni: Shin, zan gode ne, ko kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gode, to, yana godewa ne domin kansa, kuma wanda ya kafirta, to, lalle Ubangijina Wadatacce ne, Karimi |
Abubakar Mahmoud Gumi Wanda yake a wurinsa akwai wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni ina zo maka da shi a gabanin ƙyaftawar ganinka ta koma gare ka." To, a lokacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijina yake, domin Ya jarraba ni: Shin, zan gode ne, ko kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gode, to, yana godewa ne domin kansa, kuma wanda ya kafirta, to, lalle Ubangijina Wadatacce ne, Karimi |
Abubakar Mahmoud Gumi Wanda yake a wurinsa akwai wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne, Karĩmi |