Quran with Hausa translation - Surah al-‘Imran ayat 154 - آل عِمران - Page - Juz 4
﴿ثُمَّ أَنزَلَ عَلَيۡكُم مِّنۢ بَعۡدِ ٱلۡغَمِّ أَمَنَةٗ نُّعَاسٗا يَغۡشَىٰ طَآئِفَةٗ مِّنكُمۡۖ وَطَآئِفَةٞ قَدۡ أَهَمَّتۡهُمۡ أَنفُسُهُمۡ يَظُنُّونَ بِٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ ظَنَّ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِۖ يَقُولُونَ هَل لَّنَا مِنَ ٱلۡأَمۡرِ مِن شَيۡءٖۗ قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَمۡرَ كُلَّهُۥ لِلَّهِۗ يُخۡفُونَ فِيٓ أَنفُسِهِم مَّا لَا يُبۡدُونَ لَكَۖ يَقُولُونَ لَوۡ كَانَ لَنَا مِنَ ٱلۡأَمۡرِ شَيۡءٞ مَّا قُتِلۡنَا هَٰهُنَاۗ قُل لَّوۡ كُنتُمۡ فِي بُيُوتِكُمۡ لَبَرَزَ ٱلَّذِينَ كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَتۡلُ إِلَىٰ مَضَاجِعِهِمۡۖ وَلِيَبۡتَلِيَ ٱللَّهُ مَا فِي صُدُورِكُمۡ وَلِيُمَحِّصَ مَا فِي قُلُوبِكُمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ ﴾
[آل عِمران: 154]
﴿ثم أنـزل عليكم من بعد الغم أمنة نعاسا يغشى طائفة منكم وطائفة﴾ [آل عِمران: 154]
Abubakar Mahmood Jummi Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bayan baƙin cikin; gyangyaɗi yana rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rayukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da ba shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cewa: "Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne." Suna ɓoyewa a cikin zukatansu, abin da ba su bayyana shi a gare ka. Suna cewa: "Da muna da wani abu daga al'amarin da ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Ko da kun kasance a cikin gidajenku, da waɗanda aka rubuta musu kisa sun fita zuwa ga wuraren kwanciyarsu;" kuma (wannan abu ya auku ne) domin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirazanku. Kuma domin Ya tsarkake abin da ke cikin zukatanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙiraza |
Abubakar Mahmoud Gumi Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bayan baƙin cikin; gyangyaɗi yana rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rayukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da ba shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cewa: "Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne." Suna ɓoyewa a cikin zukatansu, abin da ba su bayyana shi a gare ka. Suna cewa: "Da muna da wani abu daga al'amarin da ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Ko da kun kasance a cikin gidajenku, da waɗanda aka rubuta musu kisa sun fita zuwa ga wuraren kwanciyarsu;" kuma (wannan abu ya auku ne) domin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirazanku. Kuma domin Ya tsarkake abin da ke cikin zukatanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙiraza |
Abubakar Mahmoud Gumi Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bãyan baƙin cikin; gyangyaɗi yanã rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rãyukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da bã shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cẽwa: "Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne." Suna ɓõyẽwa a cikin zukatansu, abin da bã su bayyana shi a gare ka. Suna cẽwa: "Da munã da wani abu daga al'amarin dã ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Kõ dã kun kasance a cikin gidãjenku, dã waɗanda aka rubũta musu kisa sun fita zuwa ga wurãren kwanciyarsu;" kuma (wannan abu yã auku ne) dõmin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirãzanku. Kuma dõmin Ya tsarkake abin da ke cikin zukãtanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza |