Quran with Hausa translation - Surah Al-Ahzab ayat 49 - الأحزَاب - Page - Juz 22
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نَكَحۡتُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمۡ عَلَيۡهِنَّ مِنۡ عِدَّةٖ تَعۡتَدُّونَهَاۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحٗا جَمِيلٗا ﴾
[الأحزَاب: 49]
﴿ياأيها الذين آمنوا إذا نكحتم المؤمنات ثم طلقتموهن من قبل أن تمسوهن﴾ [الأحزَاب: 49]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! idan kun auri muminai mata, sa'an nan kuka sake su a gabanin ku shafe su, to, ba ku da wata idda da za ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin daɗi* kuma ku sake su saki mai kyau |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! idan kun auri muminai mata, sa'an nan kuka sake su a gabanin ku shafe su, to, ba ku da wata idda da za ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin daɗi kuma ku sake su saki mai kyau |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun auri mũminai mãtã, sa'an nan kuka sake su a gabãnin ku shãfe su, to, bã ku da wata idda da zã ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin dãɗi kuma ku sake su saki mai kyau |