Quran with Hausa translation - Surah Muhammad ayat 15 - مُحمد - Page - Juz 26
﴿مَّثَلُ ٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۖ فِيهَآ أَنۡهَٰرٞ مِّن مَّآءٍ غَيۡرِ ءَاسِنٖ وَأَنۡهَٰرٞ مِّن لَّبَنٖ لَّمۡ يَتَغَيَّرۡ طَعۡمُهُۥ وَأَنۡهَٰرٞ مِّنۡ خَمۡرٖ لَّذَّةٖ لِّلشَّٰرِبِينَ وَأَنۡهَٰرٞ مِّنۡ عَسَلٖ مُّصَفّٗىۖ وَلَهُمۡ فِيهَا مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ وَمَغۡفِرَةٞ مِّن رَّبِّهِمۡۖ كَمَنۡ هُوَ خَٰلِدٞ فِي ٱلنَّارِ وَسُقُواْ مَآءً حَمِيمٗا فَقَطَّعَ أَمۡعَآءَهُمۡ ﴾
[مُحمد: 15]
﴿مثل الجنة التي وعد المتقون فيها أنهار من ماء غير آسن وأنهار﴾ [مُحمد: 15]
Abubakar Mahmood Jummi Misalin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga masu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu koguna na ruwa ba mai sakewa ba da waɗansu koguna na madara wadda ɗanɗanonta ba ya canjawa, da waɗansu koguna na giya mai daɗi ga mashaya, da waɗansu koguna na zuma tatacce kuma suna samu, a cikinta, daga kowane irin 'ya'yan itace, da wata gafara daga Ubangijinsu. (Shin, masu wannan ni'ima na daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wuta kuma an shayar da su wani ruwa mai zafi har ya kakkatse hanjinsu |
Abubakar Mahmoud Gumi Misalin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga masu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu koguna na ruwa ba mai sakewa ba da waɗansu koguna na madara wadda ɗanɗanonta ba ya canjawa, da waɗansu koguna na giya mai daɗi ga mashaya, da waɗansu koguna na zuma tatacce kuma suna samu, a cikinta, daga kowane irin 'ya'yan itace, da wata gafara daga Ubangijinsu. (Shin, masu wannan ni'ima na daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wuta kuma an shayar da su wani ruwa mai zafi har ya kakkatse hanjinsu |
Abubakar Mahmoud Gumi Misãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata gãfara daga Ubangijinsu. (Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya kakkãtse hanjinsu |