Quran with Hausa translation - Surah Al-Fath ayat 25 - الفَتح - Page - Juz 26
﴿هُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَٱلۡهَدۡيَ مَعۡكُوفًا أَن يَبۡلُغَ مَحِلَّهُۥۚ وَلَوۡلَا رِجَالٞ مُّؤۡمِنُونَ وَنِسَآءٞ مُّؤۡمِنَٰتٞ لَّمۡ تَعۡلَمُوهُمۡ أَن تَطَـُٔوهُمۡ فَتُصِيبَكُم مِّنۡهُم مَّعَرَّةُۢ بِغَيۡرِ عِلۡمٖۖ لِّيُدۡخِلَ ٱللَّهُ فِي رَحۡمَتِهِۦ مَن يَشَآءُۚ لَوۡ تَزَيَّلُواْ لَعَذَّبۡنَا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ عَذَابًا أَلِيمًا ﴾
[الفَتح: 25]
﴿هم الذين كفروا وصدوكم عن المسجد الحرام والهدي معكوفا أن يبلغ محله﴾ [الفَتح: 25]
Abubakar Mahmood Jummi Su ne waɗanda suka kafirta kuma suka kange ku daga Masallacin Harami, da hadaya tana tsare (sun hana ta) ta isa ga wurinta. Kuma ba domin waɗansu maza muminai da waɗansu mata muminai ba ba ku sansu ba ku taka su har wani aibi ya same ku daga gare su, ba da sani ba, (da Allah Ya yi muku iznin yaƙi), domin Allah Ya shigar da wanda Yake so a cikin rahamar Sa. Da (muminai) sun tsabbace da Mun azabtar da waɗanda suka kafirta daga gare su da azaba mai raɗiɗi |
Abubakar Mahmoud Gumi Su ne waɗanda suka kafirta kuma suka kange ku daga Masallacin Harami, da hadaya tana tsare (sun hana ta) ta isa ga wurinta. Kuma ba domin waɗansu maza muminai da waɗansu mata muminai ba ba ku sansu ba ku taka su har wani aibi ya same ku daga gare su, ba da sani ba, (da Allah Ya yi muku iznin yaƙi), domin Allah Ya shigar da wanda Yake so a cikin rahamarSa. Da (muminai) sun tsabbace da Mun azabtar da waɗanda suka kafirta daga gare su da azaba mai raɗiɗi |
Abubakar Mahmoud Gumi Sũ ne waɗanda suka kãfirta kuma suka kange ku daga Masallacin Harami, da hadaya tanã tsare (sun hana ta) ta isa ga wurinta. Kuma bã dõmin waɗansu maza mũminai da waɗansu mãtã mũminai ba ba ku sansu ba ku tãkã su har wani aibi ya sãme ku daga gare su, bã da sani ba, (dã Allah Yã yi muku iznin yãƙi), dõmin Allah Ya shigar da wanda Yake so a cikin rahamarSa. Da (mũminai) sun tsabbace dã Mun azabtar da waɗanda suka kãfirta daga gare su da azãba mai raɗiɗi |