Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 17 - المَائدة - Page - Juz 6
﴿لَّقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَۚ قُلۡ فَمَن يَمۡلِكُ مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔا إِنۡ أَرَادَ أَن يُهۡلِكَ ٱلۡمَسِيحَ ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗاۗ وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ ﴾
[المَائدة: 17]
﴿لقد كفر الذين قالوا إن الله هو المسيح ابن مريم قل فمن﴾ [المَائدة: 17]
Abubakar Mahmood Jummi Lalle haƙiƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shi ne Masihu ɗan Maryama," sun kafirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Ya nufi Ya halakar da Masihu ɗan Maryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gaba ɗaya?" Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakaninsu, Yana halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kome, Mai ikon yi ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Lalle haƙiƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shi ne Masihu ɗan Maryama," sun kafirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Ya nufi Ya halakar da Masihu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gaba ɗaya?" Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakaninsu, Yana halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kome, Mai ikon yi ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama," sun kãfirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yã nufi Ya halakar da Masĩhu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabã ɗaya?" Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, Yanã halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne |