Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 95 - المَائدة - Page - Juz 7
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡتُلُواْ ٱلصَّيۡدَ وَأَنتُمۡ حُرُمٞۚ وَمَن قَتَلَهُۥ مِنكُم مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآءٞ مِّثۡلُ مَا قَتَلَ مِنَ ٱلنَّعَمِ يَحۡكُمُ بِهِۦ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ هَدۡيَۢا بَٰلِغَ ٱلۡكَعۡبَةِ أَوۡ كَفَّٰرَةٞ طَعَامُ مَسَٰكِينَ أَوۡ عَدۡلُ ذَٰلِكَ صِيَامٗا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمۡرِهِۦۗ عَفَا ٱللَّهُ عَمَّا سَلَفَۚ وَمَنۡ عَادَ فَيَنتَقِمُ ٱللَّهُ مِنۡهُۚ وَٱللَّهُ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٍ ﴾
[المَائدة: 95]
﴿ياأيها الذين آمنوا لا تقتلوا الصيد وأنتم حرم ومن قتله منكم متعمدا﴾ [المَائدة: 95]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku kashe farauta alhali kuna masu harama*. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yana mai ganganci, sai sakamako misalin abin da ya kashe, daga dabbobin ni'ima, ma'abuta adalci biyu daga cikinku suna yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffara da abincin miskinai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi domin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Ya yafe laifi daga abin da ya gabata. Kuma wanda ya koma, to, Allah zai yi azabar ramuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwayi ne, ma'abucin azabar ramuwa |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku kashe farauta alhali kuna masu harama. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yana mai ganganci, sai sakamako misalin abin da ya kashe, daga dabbobin ni'ima, ma'abuta adalci biyu daga cikinku suna yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffara da abincin miskinai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi domin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Ya yafe laifi daga abin da ya gabata. Kuma wanda ya koma, to, Allah zai yi azabar ramuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwayi ne, ma'abucin azabar ramuwa |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa |