Quran with Hausa translation - Surah Al-An‘am ayat 19 - الأنعَام - Page - Juz 7
﴿قُلۡ أَيُّ شَيۡءٍ أَكۡبَرُ شَهَٰدَةٗۖ قُلِ ٱللَّهُۖ شَهِيدُۢ بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ وَأُوحِيَ إِلَيَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ لِأُنذِرَكُم بِهِۦ وَمَنۢ بَلَغَۚ أَئِنَّكُمۡ لَتَشۡهَدُونَ أَنَّ مَعَ ٱللَّهِ ءَالِهَةً أُخۡرَىٰۚ قُل لَّآ أَشۡهَدُۚ قُلۡ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ وَإِنَّنِي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ ﴾
[الأنعَام: 19]
﴿قل أي شيء أكبر شهادة قل الله شهيد بيني وبينكم وأوحي إلي﴾ [الأنعَام: 19]
Abubakar Mahmood Jummi Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakanina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ani domin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda labari ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙiƙa, kuna shaidar cewa, lalle ne tare da Allah akwai wasu abubuwan bautawa?" Ka ce: "Ba zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautawa Guda kuma lalle ne ni barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirka |
Abubakar Mahmoud Gumi Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakanina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ani domin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda labari ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙiƙa, kuna shaidar cewa, lalle ne tare da Allah akwai wasu abubuwan bautawa?" Ka ce: "Ba zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautawa Guda kuma lalle ne ni barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki |
Abubakar Mahmoud Gumi Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa, kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bã zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki |