Quran with Hausa translation - Surah AT-Talaq ayat 1 - الطَّلَاق - Page - Juz 28
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحۡصُواْ ٱلۡعِدَّةَۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ رَبَّكُمۡۖ لَا تُخۡرِجُوهُنَّ مِنۢ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخۡرُجۡنَ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ لَا تَدۡرِي لَعَلَّ ٱللَّهَ يُحۡدِثُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ أَمۡرٗا ﴾
[الطَّلَاق: 1]
﴿ياأيها النبي إذا طلقتم النساء فطلقوهن لعدتهن وأحصوا العدة واتقوا الله ربكم﴾ [الطَّلَاق: 1]
Abubakar Mahmood Jummi Ya kai Annabi! Idan kun saki mata, sai ku sake su ga iddarsu,* kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidajensu, kuma kada su fita face idan suna zuwa da wata alfasha bayyananna. Kuma waɗancan iyakokin Allah ne. Kuma wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to, lalle ya zalunci kansa. Ba ka sani ba ɗammanin Allah zai fitar da wani al'amari a bayan haka |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya kai Annabi! Idan kun saki mata, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidajensu, kuma kada su fita face idan suna zuwa da wata alfasha bayyananna. Kuma waɗancan iyakokin Allah ne. Kuma wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to, lalle ya zalunci kansa. Ba ka sani ba ɗammanin Allah zai fitar da wani al'amari a bayan haka |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya kai Annabi! Idan kun saki mãtã, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãshã bayyananna. Kuma waɗancan iyakõkin Allah ne. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Ba ka sani ba ɗammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bãyan haka |