Quran with Hausa translation - Surah At-Tahrim ayat 6 - التَّحرِيم - Page - Juz 28
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَأَهۡلِيكُمۡ نَارٗا وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُ عَلَيۡهَا مَلَٰٓئِكَةٌ غِلَاظٞ شِدَادٞ لَّا يَعۡصُونَ ٱللَّهَ مَآ أَمَرَهُمۡ وَيَفۡعَلُونَ مَا يُؤۡمَرُونَ ﴾
[التَّحرِيم: 6]
﴿ياأيها الذين آمنوا قوا أنفسكم وأهليكم نارا وقودها الناس والحجارة عليها ملائكة﴾ [التَّحرِيم: 6]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku kare wa kanku* (da iyalinku wata wuta makamashinta mutane da duwatsu ne. A kanta akwai waɗansu mala'iku masu kauri, masu ƙarfi. Ba su saɓa wa Allah ga abin da Ya umarce su, kuma suna aikata abin da ake umarnin su) |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku kare wa kanku (da iyalinku wata wuta makamashinta mutane da duwatsu ne. A kanta akwai waɗansu mala'iku masu kauri, masu ƙarfi. Ba su saɓa wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma suna aikata abin da ake umunin su) |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umunin su) |