Quran with Hausa translation - Surah Al-Anfal ayat 16 - الأنفَال - Page - Juz 9
﴿وَمَن يُوَلِّهِمۡ يَوۡمَئِذٖ دُبُرَهُۥٓ إِلَّا مُتَحَرِّفٗا لِّقِتَالٍ أَوۡ مُتَحَيِّزًا إِلَىٰ فِئَةٖ فَقَدۡ بَآءَ بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَمَأۡوَىٰهُ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ ﴾
[الأنفَال: 16]
﴿ومن يولهم يومئذ دبره إلا متحرفا لقتال أو متحيزا إلى فئة فقد﴾ [الأنفَال: 16]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma duka wanda* ya juya musu bayansa a yinin nan, face wanda ya karkata domin koɗayya, ko kuwa wanda ya je domin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya koma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makoma ita |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma duka wanda ya juya musu bayansa a yinin nan, face wanda ya karkata domin koɗayya, ko kuwa wanda ya je domin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya koma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makoma ita |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma duka wanda ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita |