Quran with Hausa translation - Surah Az-Zumar ayat 8 - الزُّمَر - Page - Juz 23
﴿۞ وَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ضُرّٞ دَعَا رَبَّهُۥ مُنِيبًا إِلَيۡهِ ثُمَّ إِذَا خَوَّلَهُۥ نِعۡمَةٗ مِّنۡهُ نَسِيَ مَا كَانَ يَدۡعُوٓاْ إِلَيۡهِ مِن قَبۡلُ وَجَعَلَ لِلَّهِ أَندَادٗا لِّيُضِلَّ عَن سَبِيلِهِۦۚ قُلۡ تَمَتَّعۡ بِكُفۡرِكَ قَلِيلًا إِنَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِ ﴾
[الزُّمَر: 8]
﴿وإذا مس الإنسان ضر دعا ربه منيبا إليه ثم إذا خوله نعمة﴾ [الزُّمَر: 8]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma idan wata cuta ta shafi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yana mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya juyar da cutar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yana kira zuwa gare shi a gabanin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abokan tarewa domin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji daɗi da kafircinka, a ɗan lokaci, lalle kai daga 'yan wuta ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan wata cuta ta shafi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yana mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya juyar da cutar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yana kira zuwa gare shi a gabanin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abokan tarewa domin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji daɗi da kafircinka, a ɗan lokaci, lalle kai daga 'yan wuta ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga 'yan wutã ne |